Iran ta gargadi Trump kan shisshigi a diflomasiyyarta
March 16, 2025Ministan na martani ne kan kiran da shugaba Donald Trump ya yi wa Tehran na cewa ta gaggauta yanke hulda da mayakan Houthi na Yemen, biyo bayan farmakin da Amurka ta kaddamar kan 'yan Houthin wanda ya yi sanadiyyar rayuka.
Karin bayani:'Yan Houthi sun kakkabo wani jirgi marar matuki na Amurka
Shugaba Trump ya ce Washington ta kaddamar da hare-hare kan mayakan na Houthi da ke rike da tekun Bahar Maliya da Bahar Rum har ma da gabar tekun Aden, inda suke haifar da tazgaro wajen shawagin jiragen ruwa a yankin. Wannen ne karon farko da sojojin Amurka suka kaddamar da hare-hare kan 'yan Houthi tun bayan hawan Trump shugabancin Amurka.
Karin bayani: Amurka ta kai hari kan tungar 'yan tawayen Houthi na Yemen
Ma'aikatar lafiyar Yemen ta sanar da cewa harin na sojojin Amurka ya halaka mutane 31, ciki har da kananan yara.