SiyasaGabas ta Tsakiya
Iran ta ce Amurka za ta fuskanci harin ramuwar gayya
March 31, 2025Talla
Khamenei ya sanar da hakan a jawabin da ya yi wa daukacin al'ummar kasar a sakonsa na bikin Sallah karama a birnin Tehran. Ya ce Iran a shirye ta ke wajen tunkarar Amurka idan har Trump ya aiwatar da manufarsa a kan Tehran.
Karin bayani: Trump ya yi barazanar yin amfani da tsinin bindiga kan Iran
A baya bayan nan ne dai shugaba Donald Trump ya sha alwashin yin luguden bama-bamai a Iran, idan har hukumomin Tehran suka ki amincewa da bukatar cimma yarjejeniyar nukiliya ba.