Kasashen Turai za su zauna da Iran kan shirinta na nukiliya
July 21, 2025Iran za ta sake hawa kan teburin tattaunawa da kasashen Jamus da Faransa da kuma Burtaniya kan shirinta na nukiliya a ranar Juma'a mai zuwa a birnin Istambul na kasar Turkiyya, wata guda bayan yakin kwanaki 12 da ta fafata da Isra'ila da Amurka.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ne ya bayyana hakan a safiyar Litinin, yayin da wata majiya ta diflomasiyya daga Jamus ta ce kasashen uku na aiki tukuru da Teheran don samar da masalaha mai dorewa wadda za ta ba da damar sa ido kan shirin nukiliyar na Iran.
To sai dai a gefe guda shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da wata tawaga ta mashawartan jagoran addinin Iran a fadar mulki ta Kremlin a jranar Lahadi, inda suka tattauna kan wannan batu na nukiliya.
Bayan wannan ganawa an ruwaito mista Putin na jaddada matsayin Rasha na bi ta hanyoyin diflomasiyya domin cimma matsaya kan shirin nukiliyar Iran da kuma daidaita lamura a yankin Gabas ta Tsakiya.