Iran da Amurka sun gaza sasantawa a Oman
May 12, 2025Talla
Ministan harkokin wajen Iran wanda ya tsara zaman, ya ce sun gabatar da batutuwa masu amfani kuma sahihai, a zaman sama da sa'o'i uku da suka yi da nufin cim ma matsaya
Babu dai wata nasarar da ake iya cewa an cimma kan batun na bai wa Iran damar inganta makamashinta na nukiliya da aka kwashe shekaru ana takaddama a kai.
A halin yanzu dai dukkanin bangarorin biyu, sun amince da shirin wani sabon zama a nan gaba.
Shi dai Shugaba Donald Trump na Amurka ya sha nanata cewa babu ta yadda za a kyale Iran ta mallaki makami na nukiliya, yana mai bukatar da Iran din ta lalata cibiyoyin sarrafa nukilya da take da su.
Sai dai Iran ta ce makamashin nata wanda ke na aikin farar hula ne, ba abu ne da za ta yarda da yin watsi da shi ba.