Iran ba za ta tattauna da Amurka kan mamakin nukuliya ba
March 23, 2025Iran ta ce babu wata tattaunawar da za ta yi da Amurka kan shirinta na kera makamin nukuliya har sai shugaba Donald Trump ya sauya manufarsa ta matsin lamba da yake nuna wa.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi ya ce a shirye Tehran ta ke ta mayar wa Washington martanin wasikar da Trump ya aike ma ta kan batun tattauna yarjejeniyar nukiliyar.
Karin bayani:Trump ya aike da wasikar kulla yarjejeniyar nukiliya da Iran
A farkon watan Maris da muke ciki Mr Trump ya sanar da aike wa jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei wasikar gargadi, da ke zayyana cewa hanyoyi biyu kadai zai yi amfani da su a kan Iran na cimma masalaha, wato karfin soji ko tattaunawa.
Karin bayani:Chaina, Iran da Rasha na taro kan makamashin nukiliyar Iran
A martanin da ya mayar, Ayatollah Ali Khamenei ya ce babu komai cikin tayin na Amurka face yaudara da kara lafta wa Iran takunkuman matsin lamba.