INEC ta gana da 'yan siyasa
March 23, 2011Talla
A wani mataki na tabbatar da samun nasara zaɓen da za a yi a Tarayyar Najeriya, hukumar zaɓen ƙasar wato INEC ta gana da shugabannin jam'iyyun siyasar ƙasar domin fayyace masu yadda zaɓen zai gudana a cikin watan Afrilu mai zuwa.
A wani ci-gaban kuma tsaffin manyan hafsoshin sojan Najeriya ne tare da gamayyar jami'an tsaro suka kammal wani taro a Kaduna, wanda ƙungiyar tuntuɓar juna ta dattawan arewacin ƙasar ta shirya game da tabbatar da tsaro a lokutan zaɓen.
Kuna iya sauraron sauti rahotannin da wakilanmu Uwais Abubakar Idris daga Abuja da kuma Ibrahima Yakubu daga Kaduna suka aiko mana.
Mawallafa: Uwais Abubakar Idris/Ibrahma Yakubu
Edita: Abdourahamane Hassane