INEC ta fuskanci ciƙas wajen liƙe jerin sunayen masu zaɓe
February 14, 2011Talla
A Najeriya aikin baje kolin sunayen masu kaɗa ƙuri'a da hukumar zaɓe ta ƙasa wato INEC ta yi a wannan Litinin ya fara da fuskantar matsaloli inda mafi yawan wuraren da ya kamata jama'a su je domin tantance sunayen su ba'a sami yin hakan ba. Hakan dai ya sake ta da tambayar ko shin INEC ɗin za ta iya shirya zaɓen watan Afrilun cikin gaskiya da adalci da babu maguɗi a cikinsa.
A ƙasa mun tanadar muku da rahoton da wakilin mu Uwais Abubakar Idris ya aiko mana daga Abuja.