INEC ta ɗage zaɓen ´yan majalisa
April 2, 2011Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC, ta ɗage zaɓen ´yan majalisa da ta kamata a shirya yau a faɗin ƙasar baki ɗaya.
Shugaban hukumar zaɓen Pr Attahiru Jega ya danganta dalilan da su ka sa ya ɗauki wannan mataki da rashin
isar takardun zaɓe a wasu wurare na ƙasa, wanda kuma idan babu su ba zaɓe.
Wannan mataki da hukumar ta ɗauka ya ƙarfafa tunanin masu zargin cewar da ƙyar in, a wannan karo ma, Najeriya ta ba maraɗa kunya, wajen shirya zaɓe na gari.
Tuni dai ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su ka tura masu sa ido ga zaɓen, Ƙungiyar Taraya Turai ta aika wakilai 140.
A wata sanarwar da ta hiddo tawagar Ƙungiyar Taraya Turai ta yi fatan wannan mataki ya taimaka wajen samun zaɓe mai tsafta a Najeriya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala