SiyasaAsiya
Indonesia ta kama mutane kusan 300 masu safarar kwayoyi
June 24, 2025Talla
Jami'an tsaro a kasar Indonesia sun cafke mutane 285 cikinsu har da mata 29, bisa zarginsu da aikata laifin safarar miyagun kwayoyi, bayan kwato wasu kwayoyin masu nauyin sama da rabin tan daya.
Shugaban hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi na kasar Marthinus Hukom, ya ce mutane 7 daga cikin wadanda aka kama 'yan kasar waje ne, kuma sun samu wannan nasara yayin samamen da su ka kai maboyarsu a cikin watanni biyu.
Karin bayani:China da Indonesia za su bunkasa tattalin arzikin Asiya
Hukumar yaki da muggan kwayoyi da munanan ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ayyana Indonesia a matsayin wata cibiyar safarar kwayoyi da tarin matasa ke aikatawa.