SiyasaAsiya
Indiya ta ce ba ta bukatar wani ya sulhunta ta da Pakistan
June 18, 2025Talla
Firaministan Indiya Narendra Modi ya shaida wa shugaba Donald Trump cewa kasarsa ba ta bukatar sa bakin kowa don sulhunta rikicinta da makwabiyarta Pakistan.
Mr Modi ya bayyana wa Trump hakan a tattaunawarsu ta wayar tarho ta tsawon mintuna 35, kamar yadda ministan harkokin wajen Indiya Vikram Misri ya sanar.
Karin bayani:Sarki Charles na Burtaniya ya karrama mamatan hadarin Indiya
A cikin watan Afirilun da ya gabata ne harin ta'addanci a yankin Kashmir ya kashe Indiyawa 26 'yan yawon bude ido, lamarin da ya haddasa barkewar sabon rikici tsakanin kasashen biyu abokan gaba, har aka kara samun asarar rayuka da dama, kafin daga bisani su tsagaita kai wa juna hare-hare.