Indiya da Rasha sun sha alwashin karfafa dangantakarsu
September 1, 2025Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin New Delhi da Washington, kan takaddamar sayan mai daga Rasha.
Shugabannin biyu sun tattauna bayan halartar wani taron kolin da aka gudanar a birnin Tianjin na kasar China, inda tattaunawar ta su ta mayar da hankali kan harkokin tsaro da huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
Modi ya bayyana kawancensu da Rasha a matsayin na musamman, Putin shi ma ya bayyana Modi a matsayin babban abokinsa tare da yaba kawancen da ke tsakanin kasashen biyu a matsayin abokantaka ta musamman kuma abin dogaro.
Ganawar na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya kara haraji kan kayayyakin Indiya daga kashi 25 cikin 100 zuwa kashi 50 cikin 100, a matsayin ladabtarwa kan ci gaba da sayen mai na kasar Rasha.
Karin Bayani:Putin da Modi da wasu shugabanni na halarta taro a China