Indiya da Pakistan sun yi musayar wuta
May 7, 2025A daidai lokacin da ake ci gaba da luguden wuta tsakanin India da Pakistan, kasashen duniya sun bukaci kai zuciya nesa tare da gaggauta kawo karshen yakin da kasashen biyu suka kaddamar. Kasashen biyu dai na da makamin nukiliya wanda haka ka iya zama barazana ga kowanne bangare har ma da kasashen duniya.
An dai wayi gari da luguden bama-bamai da kuma harba makamai masu linzami da rokoki tsakanin India da Pakistan da suka shafe shekaru da dama suna zaman doya da man ja, tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallakar Burtaniya a 1947.
Karin Bayani: Pakistan ta kakkabo jiragen yakin India biyar daga sararin samaniyarta
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya bukaci dukkan bangarorin dasu maida wuka cikin kube, tare da gaggauta bude sabon babin tattaunawar diflomasiyya domin warware takaddamar da ke tsakani. China wadda ke da alaka mai karfi da kasashen biyau ta sha alwashin daukar ragamar tabbatar da cewa an kawo karshen rikicin ba tare da bata lokaci ba.
Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya zargi Firaministan Indiya Narendra Modi da yunkurin fadada iko a yankin to amma Islamabad ta maida martani domin tana da ‘yancin daukar ramuwar gayya.
A yayin da yake jawabi a kafar talabijin na Pakistan, mai magana yawun ma'aikatar tsaron kasar Ahmed Sharif Chaudhry ya ce Pakistan ta yi nasarar kakkabo jiragen yakin India biyar.
Sabon rikicin dai ya samo asali ne tun lokacin da India ta yi zargin cewa Pakistan ta halaka wasu 'yan yawon bude ‘yan kasarta akalla 26 a ranar 22 ga watan Afrilu a yankin Kashmir da ke karkashin kulawar India.
A martanin da ya mayar Sakataren Harkokin Wajen India Vikram Misri ya ce sun kaddamar da farmakin ne domin murkushe 'yan ta‘addan da suka kafa sansanin a yakin Kashmir da ke karkashin ikon India.
Jamus da Turkiyya da Faransa sun shiga sahun kasashen da ke kiraye-kirayen tsagaita bude wuta, a daidai lokacin Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya kira taron gaggawa na majalisar tsaron kasar domin daukar mataki na gaba, shi ma takwaransa na India Narendra Modi ya soke dukkan tafiye-tafiyen da zai gudanar a wannan mako domin tsara jadawalin kai farmakin.
Mazauna yankin Muzaffarabad babban birnin Kashmir wanda ke karkashin ikon Pakistan na ci gaba da kauracewa yankin zuwa kan tsaunukan India.