Yunwa ta kusa kassara Zirin Gaza
May 30, 2025Kakakin Hukumar Bayar da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniyar OCHA Jens Laerke ne ya sanar da hakan, inda ya ce kaso 100 cikin 100 na al'ummar yankin Zirin Gaza na cikin babbar barazana ta shiga yunwa yana mai yin watsi da rahotannin akasin haka da Isra'ila ta sanar. Yayin wani taron manema labarai a birnin Geneva na kasar Switzerland, Laerke ya yi bayani dalla-dalla kan matsalolin da suke fuskanta wajen kai kayan agaji yankin na Zirin Gaza. Jawaban na Laerke na zuwa ne, a daidai lokacin da ministan tsaron Isra'ilan Israel Katz ya sha alwashin cewa sai sun gina kasar Yahudawan Isra'ila a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan na Falasdinun da Isra'ila ta mamaye kwana guda bayan gwamnatin Benjamin Netanjahu ta sanar da sake gina matsugunan mamaya 22 a yankin.