Najeriya: Mecece mafitar sojojin da suka aje aiki?
August 4, 2025Tsofafin sojojin dai, sun kafa tantuna guda biyu a kofara shiga ma'aikatar kudi ta Najeriya tare da yin zaman dirshen na sai abin da hali ya yi. Sojojin sun fito mazansu da matansu kan daya daga cikin manyan titunan da suka nufi tsakiyara birnin na Abuja, abin da ya haddasa cunkoson motoci a wurin da ba a bari wata mota ta tsaya. Zanga-zanga ce dai ta lumana, domin bin hakokinsu. Kasa da makwani biyu bayan tsofaffin 'yan sanda sun yi zanga-zanga a kan irin wannan batu ne, suma tsofaffin sojojin suka fito. Mafi yawansu matasa ne da sakamakon dalilai na rashin lafiya da wasu dalili na halin rayuwa suka yi ritaya daga aikin soja, domin kama wata harka a rayuwarsu bayan an biya su hakokinsu. Corporal Aliyu Abdulmalik mai ritaya tsohon sojan Najeriyar ne da aka yi masa tiyata a cikinsa a dalilin aikin sojan da a baya ya yi aiki da tsohon sojan Najeriyar nan da aka halaka Abdu Ali a dajin Sambisa, ya bayyana cewa ya shiga hali na da na sani.
Batun makudan kudi har Naira milyan 160 da shugaban Najeriyar ya bai wa 'yan matan kungiyar kwallon kafa ta Najeriyar Super Falcons, ya sake taso wa a wajen zanga-zamgar tsofaffin sojojin da suka yi ritaya amma hakokinsu suka makale fiye da shekaru biyu. Mata daga cikinsu ne dai, suka fi fuskantar kalubale. Duk wannan dauki ba dadi da ake yi a kan hakkokin sojojin Najeriyar da suka yi wa kasar aiki ya fi tayar da hankali in aka ga halin da mata da ke cikinsu suka fada, sanin cewa mata ne suka fi wahala a irin wannan yanayi kamar yadda Nwosu Florence sojar Najeriya da ta yi ritaya ta bayyana. Matsalar gaza biyan hakkokin wadanda suka yi ritaya ta zama babban kalubale daga jami'an tsaro ya zuwa farar hula, abin da ya fara kai wa ga manyan ma'aikatan gwamnati. Kwararru sun bayyana cewa, hakan na sage kashe gwiwar matasan da ke son shiga irin wadannan ayyuka.