Na yi amani Hamas na bukatar tsagaita wuta - Trump
July 8, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana da yakinin cewa Hamas a shirye take ta amince da tsagaita bude wuta a Gaza, a yayin wata liyafar cin abinci da ya yi tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu wanda ke ziyara yanzu haka a birnin Washington.
Karin bayani: Na yi imanin cewa za a cimma yarjejeniya a Gaza cikin wannan mako - Trump
A lokacin da yake ansa tamboyin 'yan jarida Trump ya ce dukannin tsare-tsaren da aka yi don tsagaita wuta a zirin Gaza na Falasdinu na tafiya yadda ya kamata, sannan kuma ya kara da cewa ba ya tunanin ko da akwai wani abu da zai iya kawo cikas.
Daga nasa bangare Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu ya bayyana cewa ya mika saunan Donald Trump ga kwamitin da ke bayar da kyautar zaman lafiya ta Nobel, duba da kokarin da yake yi a wannan lokaci na dawo da zaman lafiya a kasashe da kuma yankunan da ke fama da rikice-rikice, kautar da shugaban na Amurka ya dade yana muradin samu.