IMF: Siriya na bukatar taimakon kasashen duniya
June 10, 2025Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce kasar Siriya na bukatar tallafin kasashen duniya domin sake gida kasar. Ana dai ganin kasar bata isasshen kudin da za ta cike wagegen gibin da ta samu a dalilin zanga-zangar da ta rikide ya zuwa rikici a shekarar 2011, sakamakon wasu tsauraran manufofin gwamnatin tsohon shugabanta, Bashar al-Assad.
Karin bayani:Kasar Siriya ta Kafa dokar sake gina kasa
A kalla 'yan Siriya miliyan Shida ne suka tsere wa kasar sakamakon yakin. Alkalumma MDD sun yi nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na wadanda suke zaune a kasar na cikin kangin talauci kuma sun dogara ne a kan tallafi. A shekrar 2017, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa ana bukatar kimanin dala biliyan 250 domin sake gina Siriya, sai dai bayan hambarar da gwamnatin al- Assad, masana na cewa ana bukatar kimanin dala biliyan 400 a yanzu.