Ilimi ya tabarbare sakamakon rikici a gabashin Kwango
February 18, 2025François Siriwayo, malami ne da ya shafe shekaru yana koyarwa a makarantar sakandare ta Mambasa-Mavono, wani kauyen da ke kudancin Lubero. Amma tsanantar da fada ke yi a gabashin Jamhuriyar Dimukuariddyar kwango ya sa shi kaurace wa gidan shi, inda ya samu mafaka a garin Butembo da ke arewacin garinsu. Ya ce: " A makarantarmu, an shafe watanni ba tare da gwamnatin Kwango ta biya mu albashi ba, saboda haka ina rayuwa ne hannu baka, hannu kwarya. "
Karin bayani: Shugabannin Afirka sun bukaci tsagaita wuta a DRC
Siriwayo ya nemi mafaka a wannan gari da ke Arewacin Kivu ne bayan da 'yan tawayen M23 suka kwace kauyensa a watan Disamban bara. Tun daga wannan lokaci ne, ya rasa aikinsa kuma ba shi da labarin halin da dimbin dalibansa ke ciki. Ya kara da cewa: “Dalibaina sun warwatse, da yawa daga cikinsu ba su ci gaba da karatunsu ba saboda suna gudun hijira, yakin yawatsa mu gaba dayanmu. Ban san yanayin da kauyenmu ke ciki ba. Sai dai na samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun mamaye wasu makarantu."
Makarantun 190 na rufe a garin Lubero
An rufe yawancin makarantun firamare da sakandare a yankin Kitsumbiro da ke kusa da cibiyar Lubero, bayan hare-haren da 'yan tawayen M23 da suka yi nasara a karshen 2024. Sai dai Roger Katekere, wani jami’in hukumar kula da makarantar yankin, ya nuna bakin cikinsa game da yawan yara da suka daina samun ilimi., inda ya ce: “An kiyasta cewa makarantu 190 cikin 255 ba sa aiki a wannan yanki. Kama daga Kaseghe, Hutwe, Alimbongo, Vutsorovia, Matembe da ka zama garuruwan da ke kan hanyar Kirumba zuwa Lubero, duk makarantun ba su ma fara zangon karatu na bana ba."
Karin bayani: Tabarbarewar jinkai a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Tun bayan hare-haren bama-bamai na baya-bayan nan da 'yan tawayen M23 suka kai a sansanin sojojin Kwango, iyalai da dama sun kama hanyar gudun hijira zuwa tsakiyar Lubero. Shi ma ministan tsaron Kwango ya je fagen daga a kudancin Lubero, a ranar Talata 11 ga watan Fabrairun 2025, domin kara kwarin gwiwar ga sojojin kasar.
Bukatar ceto ilmin yara a DR Kwango
Amma a Lubero, Joslyne Nzenze na kungiyar "Rien sans les femmes" ta nuna takaici game da yadda yaki ke ci gaba da dakile ayyukan neman ilimi na yara. Ta ce: “ Muna ganin yara da yawa ba su zuwa makaranta, suna yawo a kan tituna musamman a tsakiyar garin Lubero. A gare mu, abin takaici ne, domin ilimin yaran yana cikin hadari. wai shin wace irin kasa ce za mu samu a gobe? a hakika bala’i ne! Idan an rufe makarantu 190, akwai matsala domin kowace makaranta yara nawa ta kunsa? Kuma ina wadannan yaran suke? Ya kamata hukumomi su yi tunani kan yadda za a ceto duk yaran da suka kasance a yankunan da ake rikici. "
Karin bayani: Rikicin Jamhuriyar Kwango da Ruwanda ya yi kamari
A cikin wata sanarwa da aka fitar a baya-bayannan, gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta yi tir da "cin zarafin da Ruwanda da 'yan barandanta suke yi," wa makarantu a gabashin kasar, duk da tsagaita bude wuta da aka cimma a taron hadin gwiwa na SADC da EAC a Tanzaniya.