Ikon siyasa a Rasha
September 24, 2011A wani matakin da ke fayyace rawar da kowannensu ke takawa a fagen siyasar Rasha, wanda kuma ya kawo karshen hasashen da aka shafe watanni da dama ana yi, Framinista Vladimir Putin ya gabatar da shugaban kasa Dimitry Medvedev a matsayin wanda zai jagoranci 'yan takarar jami'yyar a zaben majalisar dokokin da za'a gudanar ranar 4 ga watan Disemba a kasar. Putin ya fadi haka ne a taron shekara-shekara na jam'iyyar shugabanin biyu ta United Russia Party.
Jim kadan bayan haka ne kuma shi ma Medvedev ya gabatar da nasa jawabin inda ya shawarci taron cewa Putin ya tsaya a matsayin dan takarar shugabancin kasar a zaben shugaban kasar da za'a gudanar a watan Maris na shekara mai zuwa. Wannan sanarwar dai ta nuna amincewar Medvedev ya sauka daga kujerar shugabancin kasar bayan ya yi wa'adi daya a mukamin ya kuma mika ragamar ga Frime Minista Putin wanda ya yi wa'adi biyu a nasa mukamin daga shekarar 2000 zuwa 2008.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Halima Balaraba Abbas