Dambarwar masarautar Kano ta sake hana hawa
June 6, 2025Wannan shi ne Idi na hudu da ba a hawan Sallah a Kano kamar yadda aka saba yi a masarautun Daular Usmaniya. Bayan Khudubar Sallar Idin, Sarki ya yanka ragunansa, sannan hakimai suka koma fadar Masarautar Kano a motocinsu kafin Sarki Muhammadu Sanusi ya fita a motarsa zuwa fadar.
Kade kade da bushe bushen da aka rika yi don tunawa jama'ar da ta taru a lokacin da Sarki ke komawa fadarsa, yadda aka saba yin shagulgulan Sallar.
Wani bangaren bikin Sallar da a yanzu yake tashe shi ne daukar hotuna a filayen Idi don turawa da sakonnin fatan alkhairi ga ‘yan uwa da abokan arziki. Na tambayi Mal Yahya wani matashi da aka yi masa hoton Sallah ko nan da ma ya saba yin Sallar Idi.
"Nan na saba zuwa kuma ina jin dadin yin Sallah a nan wurin. Eh to gaskiya dai ina da wurin da zan je amma duk shekara na kan tsaya dai wajen Sarki na dan yi kallon Sarki.To amma kuma a wannan akwai inda za ni."
Shi kuwa Mal Bashir Khalil yana daga cikin magidantan da ya yi Sallar tare da 'ya'yansa.
"Sallah Alhamdu Lillahi.Allah mun gode ma.Allah ka kara maimaita mana yadda muka zo wannan lokaci lafiya."
Mutane da dama suna ta dokin ganin hawan Sallah na farko tun bayan da Hukumar Raya Ilmi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta zabi hawan Sallar Masarautar Kano ya koma karakashin kulawarta.Sai dai dambarwar Masarautar tsakanin sarkuna biyu Malam Muhammad Sanusi na biyu da kuma Alhaji Aminu Ado Bayero inda kowanne yake ikirarin shi ne Sarki, ya hana..