Human Rights ta bukaci binciken kisan mutane a Burkina Faso
March 15, 2025Kungiyar kare hakkin 'dan adam ta duniya Human Rights Watch ta yi kira ga gwamantin mulkin sojin Burkina Faso da ta gudanar da bincike na gaskiya kan kisan gillar da ake zargin dakarun sojin kasar da yi wa tarin fararen hula, mafi akasarinsu mata da kananan yara da kuma tsofaffi a birnin Solenzo.
Babbar jami'ar kungiyar mai nazari a yankin Sahel Ilaria Allegrozzi, ta ce faya-fayen bidiyon da suka samu sun nuna yadda aka watsar da gawarwakin mutanen hannayensu a daure cikin mummunan yanayi na rashin imanin da aka aikata musu, a don haka tilas mahukuntan kasar su gaggauta kaddamar da binciken kwakwaf don gano gaskiyar abin da ya faru.
Karin bayani:Sabon babi a yaki da ta'addanci a Sahel
Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa dakarun sojin kasar bisa hadin gwiwar kungiyoyin 'yan bindiga, sun halaka dangi guda na fulani daga ranar 10 zuwa 11 ga watan din nan da muke ciki.
Karin bayani:'Yan bindiga sun halaka mutane kusan 20 a Jamhuriyar Nijar
Kusan shekaru goma kenan da Burkina Faso ta fada cikin yanayin matsalolin tsaro na hare-haren ta'addancin masu ikirarin jihadi, wadanda suka tsallaka zuwa makwabtan kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar.