Hukumar tsaro ta SSS ta yi taron manema labarai a Abuja
March 29, 2012Hukumar tsaro ta kasa a Najeriya wato SSS ta gabatar da gungu wasu matasa su bakwai wadanda suka shahara wajen garkuwa da 'yan kasashen waje a cikin kasar, bayan da suka kame wani balarabe da niyyar samun kudi a wajensa, abinda ke nuna ci gaba da yunkurin dakile masu wannan mummunan dabi'a da hukumomin kasar ke yi.
Wadanan matasa da dubu ta cika a kansu, bayan da suka yi garkuwa da wani dan asalin Hadadiyar Daular Larabawa da mai suna Mohammed Khamis Majed Ismail Al Ali ,wanda bayan da suka yaudare shi da sunan gudanar da cinikayya mai tsoka inda da isowarsa Najeriya suka yi garkuwa da shi a kauyen Aborigun da ke jihar Osun har na tsawo kwanaki 60.
Yunkurin samun kudi ta hannun balaraben ta ci tura duk da amfani da kamfani na jabbu da suka yi wato Finoche Investment, abinda ya sanya gungun matasan da suka hada da Ojo Ajibade mai shekaru 22 da Jalili Ajagunbade da ke da shekaru 33 suka tasa keyar Khamis tare da sakinsa a birnin Badin don ya kama gabansa. Kakakin hukumar tsaro ta Najeriyar Marilyn Ogar ta bayyana yadda suka dauki wannan lamari a dai dai lokavin da ake ci gaba da koken tabarbarewar rashin tsaro a cikin kasar.
Ta ce tun daga lokacin da muka ji labarin sace Mohammed Khamis ne muka zabura wajen binciken inda a ranar 19 ga wata wadanda suka sace shi suka sake shi a garin Badin, inda a ranar 20 ga wata muka samu nasara cafke wadanan mutanen, kuma binciken da muka yi sun tabbatar da aikata wannan laifin inda daya daga cikinsu Khashim ya dauke shi a machin, inda a can ne aka sake shi.
Ganin cewar mutanen bakwai da aka gabatarwa yan jaridu dukkaninsu sun sanya kaya iri guda ne ya sanya tambayar daya daga cikinsu yadda suka aikata wannan laifi.
Dayansu yace mu ma'aikata ne a a wani kamfani maigidanmu ne ya kawo shi mu ajiye kuma da muka gaji da jira babu labarinsu muka saki wannan mutumin.
Wannan ya sanya tambayar kakkakin hukumar yadda a mafi yawan lokuta ake gabatar day an kore maimakon zahirin wadanda suka aikata laifin inda Marylyn Ogar ta bayyana cewa
Tace ai ba batun wwai ana amafani da wasu bane idan har basu da hallaya ta aikata miyagun laifuffuka ai babu wanda ya kamata ya yi amafani das u, kame irin wadannan muhimmin sako ne ga alumma, don masu aikata laifi a cikin alumma suje kwanici sitin aka yi ana tsare da wannan mutumin a cikin alumma.
Ci gaba da samun masu aikata miyagun laifuffuka irin na sacewa da ma garkuwa da jama na zama babban kalubalen rashin tsaro a Najeriya domin koda a watan Janairu an sace wani dan kasar Jamus Edger Raupach wanda har yanzu babu labarin inda yake abinda yasa Dr Sadeeq Abba masanin kimiyyar siayasa bayyana cewa lamari ne mai cike da illoli ga kasar.
Matsaloli na aiyukan ta'adanci sace jama'a da ma garkuwa das u na ci gaba da zama babban kalubalen da ke fuskantar harkar zamantakewa siyasa da ma tsaron Najeriya da ake ci gaba da gwamnati ke ci gaba da ikirarin tashi tsaye don shawo .
Mawallafi: Uwais Abubakar Idriss
Edita: Yahouza Sadissou Madobi