Hukumar tallafin abinci ta MDD za ta rage ma'aikatanta
April 28, 2025Talla
Shugaba Donald Trump ya matsa kaimi wajen rage gudumawar da Amurka ke ba MDD da hukumominta tun bayan komawarsa fadar White House, lamarin da ya haifar da rudani, kasancewar a baya Washington ce ke bayar da gudummawar kasafin kudi mafi yawa.
WFP ita ce babbar kungiyar agaji ta duniya, wadda aka kafa a shekarar 1961 da alhakin kare karancin abinci da matsananciyar yunwa a duniya, kuma ke taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matsalar abinci a wuraren da ake yaki kamar Sudan da sauran yankunan da suka fuskanci bala'i.
Kafin wannan matakin, hukumar tana da ma'aikata 23,000 da ke aiki a kasashe 120.