Hukumar Standard & Poor's ta rage darajar biyan bashi ga wasu ƙasahen Turai
January 14, 2012Hukumar da ke tantance matsayin ƙimar ƙasashe ´na biyan basusuka Standar & Poor's ta ta rage darajar ƙasar Faransa na biyan bashi; wannan al 'amari na bazata da ya zo yayin da ya rage ƙwanaki 100 a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Faransa na zaman wani babban koma baya ga shugaba Nikolas Sarkozy.
A cikin ƙasashen Turai ƙasar jamus i'ta ka dai ce ta ke riƙe da matsayin mai daraja tare da ƙasahen Hollande da Filand da kuma Luzambak ya yin da portugal ta zo ta ƙarshe.Fraministan ƙasar Francois Fillons wanda ya maryar da martanin bayan taron gawgawa da ya gudanar tare da shugaban ƙasar ya ce ba hukumar ce ba ke tsara siyasar ƙasar Faransa.ministan kuɗi na faransar Francois Baroin ya ce ko kaɗan ba zasu sake ƙaddamar da wani shirin tsuke bakin aljihu ba bayan wanda suka yi a shekara bara.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman