Hukumar Moody's ta rage ƙimar wasu ƙasashen Turai
July 24, 2012Talla
A cikin wata sanarwa da ta baiyana hukumar ta Moody's ta ce matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a cikin wasu ƙsasahen nahiyar Turai ta bar taɓo akan tattalin arzikin ƙasahen guda ukku.
Wanda tun can da farko ta saka su acikin jerin ƙasashen da suka tsira daga faduwar darajar,da yake mayar da martanni ministan kuɗi na kasar jamus ,ya ce har yanzu Jamus ta na da ƙarfin da ta ke da shi na ɗorewar al'ammuran tattalin arziki,sannan kuma ya zargi hukumar ta Moody's da yin hasashen akan gajeren lokaci a maimakon yin hangen nesa.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh