Hukumar lafiya ta koka da halin da al'ummar Gaza ke ciki
May 26, 2025Talla
A wani taron manema labarai a Geneva, darektar yankin Gabashin Mediterrenean Hanan Balkhy ta ce, fiye da makonni 11 babu wasu motocin hukumar WHO da ke shiga Gaza don tallafin kiwon lafiya, duk kuwa da barin daidaikun motocin agaji shiga yankin cikin 'yan kwanakin nan.
Ta ce suna cikin damuwa a kan yadda mutane ke cikin hali na tagayyara da bukatun jinya, amma babu abunda za su iya yi, duk da cewa manyan motoci 51 dauke da kayan jinya suna kan iyaka.
Kimanin motocin dakon kaya 400 aka amince su shiga Gaza, amma ya zuwa yanzu 115 ne kacal suka samu damar isar da kaya, kuma babu daya daga cikin motocin da aka bari ya je arewacin kasar da dakarun Isra'ilan suka killace.