Hukumar INEC na shan suka
January 17, 2011Yanzu haka a kusan faɗin Tarayyar Najeriya ana fiskantar matsaloli a game da yin rijistar 'yan ƙasar, waɗanda suka cancanci jefa ƙuri'a a zaɓuɓɓuka masu zuwa, wanda ƙasar ke shirye-shiryen tunkara a 'yan watanni masu zuwa, ko da yake hukumar zaɓen ƙasar na nuna cewa ta na ɗaukar matakai a kan waɗanan matsalolin kamar yanda wakilin mu a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya Uwais Idris ya aiko mana har yanzu ba kai ga shawo kann matsalar ba
Yanayin rijista a Gombe bambanci
A can jahar Gombe ma kazalika ana ci gaba da samun tangarɗa ga aikin na rijista, inda kamar yadda wakilin mu a yankin Amin Sulaiman Muhammad ya shaida mana har kawo yanzu mutanen da aka yiwa wannan rejista ba su taka kara ba,
Kuna iya sauraron sautin rahotonnin nasu a ƙasa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal