UNCTAD za ta rage ma'aikata saboda matsalolin arziki
June 18, 2025Hukumar cinikayya da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya da ke da alhakin taimaka wa kasashe masu tasowa samun damar shiga harkokin tattalin arzikin duniya, na fuskantar mummunan mataki na tsuke bakin aljihu, a matsayin wani bangare na sauye-sauyen da aka samu sakamakon raguwar kudaden tallafin da kasashen duniya ke bayarwa.
Babbar sakatariyar hukumar Rebeca Grynspan, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, ta damu da ganin ayyukan hukumar za su fuskanci cikas, yayin da bukatar ayyukan ke karuwa, kuma a daidai lokacin da kasashe ke neman bayanai kan tasirin karin harajin da shugaban Amurka ya dora wa kasashe.
Dangane da kasafin kudin hukumar ta UNCTAD na 2026, Grynspan ta ce tare da tawagarta sun ba da shawarar soke mukamai 70, daga jimlar adadin mutane 500 ciki har da masu ba da shawara, da kusan mukamai 400 na dindindin.
Ya zama wajibi wa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya kamar UNCTAD, su rage kudaden da suke kashewa, biyo bayan matsaloli na tattalin arziki da Amurka ta haifar, wacce ke ba da kusan kaso daya bisa hudu, na kudaden gudanawar hukumar ta duniya.