SiyasaGabas ta Tsakiya
Houthi ta kama jami'an MDD da ke yi wa Isra'ila leken asiri
September 4, 2025Talla
'Yan tawayen Houthi na Yemen sun sanar da kama jami'an Majalisar Dinkin Duniya su 11, bisa zarginsu da yi wa Isra'ila da Amurka leken asiri.
Kamen ya biyo bayan kisan da Isra'ila ta yi wa firaminista Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi da ministocinsa 9, hadi da wasu mukarrabansa 2, a ranar Alhamis da ta gabata.
Mutanen da aka kama sun hada jami'an hukumar samar da abinci ta duniya, da na asusun kula da da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.
Karin bayani:'Yan Houthi a Yemen sun tabbatar da kisan firaministansu a harin Isra'ila
Ko a ranar Asabar sai da jami'an tsaron kasar suka cafke mutane da dama da ake zargi da hada baki da Isra'ila, kamar yadda suka tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP.