Japan: Shekaru 80 da harin Hiroshima
August 6, 2025Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kasashe ke tserereniyar mallakar manyan makamai, ciki har da makaman nukiliya. Tsakanin mutane dubu 90 zuwa dubu 136 ne suka rasa rayukansu nan take ko kuma suka mutu daga bisani, sakamakon munanan raunuka a lokacin da Amurka ta harba makamin kare dangi a Hiroshima a ranar shida ga watan Agustan 1945. Shekaru 80 da suka gabata, lokacin Setsuko Thurlow na da shekaru 13 a duniya kuma ta bayar da labarin firgicin da ta samu kanta a ciki a ranar da ta ce ta canza komai a rayuwarta.
Karin Bayani: Taron G7 na tunawa da Hiroshima
Iyayen Thurlow sun tsira daga harin makamin nukiliyar, amma 'yar uwarta da 'yar yayarta sun mutu kwanaki kadan bayan fashewar makamanin kare dangi a Hiroshima. Amma kasancewar Japan ba ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba bayan harin na Hiroshima, gwamnatin Amurka ta yanke shawarar jefa makamin nukiliya na biyu a birnin Kokura mai tashar jiragen ruwa. Sai dai sakamakon rashin kyawun yanayi, jirgin yakin ya canza akalarsa zuwa Nagasaki a ranar tara ga watan na Agustan 1945 din. Dubban mutane ne suka mutu kuma jim kaɗan bayan haka, yakin duniya na biyu ma ya kare a Asiya.
Dubun-dubatar wadanda suka tsira daga hare-haren biyu sun samu illa a rayuwarsu, kamar konewa da ciwon daji. Saboda hake ne Setsuko Thurlow mai fafutukar zaman lafiya ta sadaukar da rayuwarta wajen yaki da makaman kare dangi, inda ta zama jigo a cibiyar ICAN ta kasa da kasa da ke neman kawar da makaman nukiliya da ta samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a 2017. Tun daga 1947, ana kada kararrawar zaman lafiya a Hiroshima da karfe takwas da mintuna 15 na safe a ranar shida ga watan Agusta. Ana kuma gudanar da bikin tunawa da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, a harin na nukiliya. Shi kuwa magajin gari ya yi kira da a kawar da makaman nukiliya tare da yin kira ga zaman lafiya a duniya baki daya.
Karin Bayani: Japan: Shekaru 72 da harin Amirka a Hiroshima
A wata hira da DW masanin tarihin soja kuma masanin tarihin kasar Japan Takuma Melber na jami'ar Heidelberg, ya ayyana bikin tunawa da tashin bama-baman a matsayin "bikin al'adu mai muhimmanci" ga al'ummar kasar. Bayan yakin duniya, tsofaffin abokan hamayya wato Japan da Amurka sun kara kusantar juna, sai dai bangaren Amurka bai taba neman afuwa dangane da harin makaman kare dangi da ya kai ba. Duk ma da cewar Japan ba ta cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, amma dai ta kasance abokiyar tafiya. Saboda haka ne kasar Amurka ke kare ta daga hare-haren abokan gaba, saboda Japan ba ta mallaki makaman nukiliya ba. A halin yanzu ma kusan sojojin Amurka dubu 54 ne suke jibge a Japan din, domin bayar da gudummawa ga tsaron kasar.