Masarautar Hausawa ta unguwar Agege da ke jihar Lagos a kudu maso yammacin Najeriya masarauta ce mai tarihi sosai.Alhaji Musa Muhammadu Dogon-Kadai shine sarkin Hausa na unguwar Agege a yanzu. DW ta yi tattaki zuwa fadarsa inda ta tattauna da shi kan yadda hausawan Lagos ke kokarin raya al'adun Bahaushe da kuma sauran batutuwa.