Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar, ya ce har yanzu suna kokarin shawo kan kasashen da suka balle daga ECOWAS don su dawo, duk da wa'adin ficewarsu ya cika. Ministan ya kuma fadi dalilin da ya sa suke sa in sa da gwamnan Bauchi kan dokar haraji.