Tattalin arziki
Matashi mai noman albasa a Sakkwato
May 4, 2022Talla
Matashin mai suna Hassan Muhammad Ladan ya shafe kusan shekaru biyu yana gudanar da noman rani na albasa, inda ya bayyana cewa noman ya zame masa garkuwa. Sai dai matashin ya ce duk da irin nasarorin da yake samu a noman, to akwai tarin kalubale da ke zame masa karfen kafa ga burin da yake son cimma.