Hatsarin wutar daji a Rasha
August 12, 2010Talla
Wutar daji dake ci gaba da yaɗuwa a ƙasar Rasha ta isa wuraren dake da sinadarin nukiliya, inda aka samu wata babbar masifar sinadarin a shekara ta 1986. Wani jami'in kashe gobara ya tabbatar da isar wutar, inda yace sun dai samu kashe wutar, a ɗaya daga wurin dake da sinadarin. Masana sun bayyana fargabar cewa turniƙin sinadarin zai yiya kasancewa wani babban haɗari ga bil'adama, ko dayake ana zaton turniƙin bazai yi yawa ba. A babban birnin ƙasar ta Rasha wato Moskow, iska mai ƙarfi dake kaɗawa ta taimaka wajen kawar da hayaƙin da ya turniƙi birnin.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu