SiyasaJamus
Hatsarin kwale-kwale ya hallaka gomman mutane a Zamfara
August 30, 2025Talla
Kwale-kwalen dake dauke da su ya nutse a wani rafi dake garin birnin Magaji a kokarin tserewa wani harin da 'yan bindiga suka kai musu.
Maharan da suka yi wa garin kawanya sun bude wuta da harbin kan mai uwa da wabi wanda ya tarwatsa al'umma. Kamar yadda hakimin birnin Magaji Alhaji Maidamma Dankilo ya tabbatar.
Jihar Zamfara na fama da hare-haren 'yan bindiga wanda ko a makon da ya gabata a wani gari dake kusa da birnin Magaji sun kashe mutane biyu suka kuma yi awon gaba da sama da wasu 100 zuwa cikin daji.
Sama da hare-haren satar mutane domin neman kudin fansa 50 ne jihar ta Zamfara ta gani daga watan Yuni shekarar 2024 zuwa Yulin shekarar 2025.
Karin bayani :Rundunar Sojin Najeriya ta kashe 'yan bindiga 100